Hadarin amfani da GB whatsapp

 

Da farko 'yan uwa yana da kyau musani GBWhatsApp "Third-party application" ne. Idan akace "Third-party application" ana nufin dukkan wani abu wanda ba asali daga kamfanin ba. GBWhatsApp wasu ne suke modding asalin WhatsApp inda matsalar yake yanzu ire-iren waÉ—annan application irin GBWhatsApp sun yawaita harma da na masu mummunar manufa dan haka asan irin GBWhatsApp dinda za'ayi amfani dashi inma yazama dole. 

Daya daga cikin babbar matsalar GBWhatsApp shine "Satar bayanan mutane"  wannan muna daukar sa ba akamin komai ba saboda a ganinmu baya shafar mu a zahiri sai dai a hakikanin Gaskiya yana shafar mu a baÉ—ini. A lokacin da kake Installing GBWhatsApp a wannan lokacin application din zai nemi izinin satar duka wani bayanai dake wayar. Da zaran mukayi "Allow" dinnan na nufin mun yarda mun amince su dauki komai a wayar. Wadannan bayanan da suke sata sun hada da Contacts (Lambobi dake wayar), Files (Hotuna, Videos, Wakoki da sauransu), Call Lig (Bayanan kira), Messages (Sakonin kar ta kwana), da sauransu. 

Idan muka dauki iya contacts kadai zamu iya gano matsaloli da ke tattare da wannan sanin kanmu mafi yawan lokuta muna saving details dinmu na asusun banki da irin password da sauransu akan contact na wayarmu saboda kar mu manta, idan GBWhatsApp suka saci duka contacts dake wayoyin mu kenan harda irinsu Account numbern mu, BVN dinmu ATM PIN da sauransu kila ma harda details na wasu mutane da mukayi saving kenan duk zasu iya gani su kwashe. Shin baka taba mamakin kana zaune kaga an turo maka message a wani number, ko a kiraka? Ko kuma ma akiraka a fadamaka kaine wane kaza da kaza wanda ya kirakan yayi tamkar ya sanka? Kila ma ya fadamaka tsaf bayananka na banki? Shin kataba tambayar kanka ina yasamu lambarka? Alhali baku da hadi dashi ta nesa ko ta kusa? Ire iren wadannan applications din na daga cikin abinda ke taimaka musu wajen samun bayanai akanka ko na waninka sannan yanzu haka akwai wadanda zaka iya siyan phone number na mutane dubu goma in kanaso a wajensu, haka email da sauransu shin a ina suke samun wadannan lambobin alhali basa aiki da kamfanin? Ire iren wadannan applications a shi suke samu. Sannan kada mu manta sun accessing messages din mu wanda sanin kowa transaction alert a message yake zuwa kenan suna iya samun bayanan mu har yanzu. Misa ke  daukar wata misalin yanzu ace nine nayi GBWHATSAPP na sake mutane dubu biyu sukayi downloading idan sukayi installing application din na dauko min contacts dinsu ya turomin idan misali mukace kowane mutun daya akwai contacts É—ari a wayarsa guda nawa zantara? Anga kenan lallai akwai hatsari. 

Muzo mudauki Files a misaki na gaba, musamman a wannan zamanin akwai abubuwan da mukeyi sannan mu ajiye a wayoyin mu wanda hatta iyayenmu bamason musani akwai ire iren wannan abin a wayoyin mu munfiso yazamto sirri ne na mu kadai shin ya ake tunani ace mutun ya samu wannan abin? Kamar yadda na bada misali ne da farko ace nine developer na GBWhatsApp gashi inada bayanai na mutanen unguwarku wanda kila akwai wani abu da kakeso kasani a wayarsa zaka iya zuwa kasameni kila muyi ciniki in siyarmaka a misalance kenan. Shin wannan babu hadari acikin? Lallai akwai.


Post a Comment

Post a Comment (0)

Previous Post Next Post